Tehran (IQNA) Masallacin Murad Agha da ke birnin Tripoli babban birnin kasar Libiya ya cika shekaru 500 da kafuwa, kuma gado ne mai kima daga mulkin daular Usmaniyya a wannan kasa. Har ila yau, wannan masallacin ya kasance wata alama ce ta tsayin daka da al'ummar Libiya suka yi wa mamaya na Spain a karni na 16.
Lambar Labari: 3488342 Ranar Watsawa : 2022/12/15